2021 Kisan kiyashin Kebbi

Infotaula d'esdeveniment2021 Kisan kiyashin Kebbi
Iri harin ta'addanci
Kwanan watan 3 ga Yuni, 2021
Wuri Kebbi
Ƙasa Najeriya
Adadin waɗanda suka rasu 90

A ranar 3 ga watan Yunin shekarar 2021, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a ƙauyuka takwas a jihar Kebbi, arewa maso yammacin Najeriya, inda suka kashe akalla mutane 90.

Faruwar Lamarin

An fara kai harin ne da karfe 3 na rana; ‘ Yan bindigar da suka hau babura sun kai farmaki kauyukan Koro, Kimpi, Gaya, Dimi, Zutu, Rafin Gora da kuma Iguenge.[1][2] ‘Yan bindigar sun fito ne daga jihohin Niger da Zamfara da ke makwabtaka da Najeriya, sun kuma yi awon gaba da shanu tare da lalata amfanin gona.[1][3][4]

Manazarta