Assodé gari ne a tsaunukan Aïr da ayanzu ke a Arewacin Nijar. An kirkiri garin ne a karni na shadaya, da dadewa shine birni mafi muhimmaci tsakanin Abzinawa dake a yankin. Sakamakon rikicin da akayi na Kaocen a 1917 birnin ya durkushe kuma jama'a suka kaurace ma garin. A yanzu gineginen garin sun zama wani waje na yan yawon bude idanu a Nijar.