Beguwa
Beguwa | |
---|---|
organisms known by a particular common name (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Hystricognathi (en) |
Taxon known by this common name (en) | New World porcupine (en) da Old World porcupine (en) |
Beguwa ana kiranta da turanci da (porcupine) tana ɗaya daga cikin dabbobi masu ƙaya irin su bushiya da sauransu. Sai dai ita tata ƙayar tasha banban da sauran domin ita ƙayar ta tana amfani da ita wajen kare kanta daga harin waɗansu dabbobin waɗanda suke farautar nama. Ita dai beguwa kusan kashi biyu ce kuma ko wane ɓangare kusan baya kama da junansu. Ana samun beguwa a Nahiyar Asiya da kuma wani yankin Afirka sai dai beguwa Afirka sunfi girma kamar yadda bincike ya nuna.[1][2][3].
Girma da tsawon beguwa
Mafi yawan beguwa tsawon su baya wuce daga santimita 60-90 sai dawowa ƙasa sai kuma nauyin ta yana kaiwa har 24 shima zuwa ƙasa da hakan.
.
Siffa da nau'in beguwa
Beguwa tana da ƙaya a bayanta ƙaya kuma mai tsawo da tsini gami da dafi, haka kuma beguwa akwai mai toka-toka, sai mai ruwan ƙasa da kuma farar beguwa. Jinsin beguwa kusan kala 58 ne kamar yadda masu bincike suka faɗa, haka takan hau bishiya
Abincin beguwa
Beguwa tana cin ganyaye haka kuma tana cin ciyawa kore shar, beguwa takan hau saman bishiya don neman abinci. Sai kuma beguwa takan ci ƙananan ƙwari irin su cinnaka fara Gara da dai sauransu.
Ƙayar beguwa
Tsinin ƙayar beguwa kala-kala ne ya danganta da jinsin/nau'in ta waɗannan ƙayoyin suna fitowa akan beguwa da bayanta da dai sauran sassan jikin ta da ƙaya take fitowa. Ƙayoyin beguwa sukan zubo a cikin lokaci-lokaci da kuma wani lokaci idan ta girgiza jikin ta, haka kuma takan kaiwa abokan gabanta hari da waɗannan ƙayoyin ta ɗin tana harbi dasu daga waje mai nisa duk da wasu suna ganin ba gaskiya bane a taƙaice tana kare kanta da waɗannan ƙayoyin har maharba takan harbe su da ƙayoyin ta. Haka waɗannan ƙayoyin akwai waɗansu anti-bayotik (antibiotics) waɗannan anti-bayotik suna taimaka wa beguwa a lokacin da ta samu wani rauni.
.
Naman Beguwa
Duk da ba kasafai ba ake cin naman Beguwa ba a ɗabi'un yammaci (Western culture) sai dai a gabashin Asiya inda yawancin mutanen wannan yankin suka ɗauka beguwa (naman ta) a matsayin Abinci. Haka idan muka dawo a irin Afirka masu maganin gargajiya suna amfani da ƙayoyin ta wajen yin tufafi da kuma ado da kwalliya irin ta ƴan gargajiya. Haka a waɗansu yankuna na Amirka suma na gargajiya suna amfani da ƙayoyin ta wajen yin hula da sauransu. Sai kuma a zamanance ana amfani da ita wajen yin jakar leda, kuben wuƙa sai kuma mata a ƙauye suna amfani da ƙayar beguwa wajen tsifar gashi (suma) a lokacin da suke so su canja kitso.
Mazaunin Beguwa
Beguwa tafi zama a gurare masu zafi irin yankuna masu zafi a Asiya da kudancin yurop (southern Europe) Afirka da Arewa da kudancin Amirka. Beguwa tana rayuwa ne a daji a cikin kurmi, ko kuma a sahara da kuma irin gefen tsaunuka (hills) da duwatsu, don anyi bincike beguwa tana hawan tsauni sama da mita 3,700 (kusan 12,100ft) ta tsawo kenan. Beguwa tana fita ne da dare don kiwo da neman abinci, Kodayake akwai wani lokaci takan fita har da rana. Maharba Mafarauta' suna harbo beguwa daga daji da kayan farauta da sukeyin farauta dasu irin su bindiga, takobi, Adda da sauran su saɓanin sauran dabbobin daji suda har da sanda akan kashe su, amma ƙwararrun maharba (wato masu asiri) sukan shiga har ramen ta su kamota, su yankata.
Manazarta
- ↑ "Ka san wuta ba ta hallaka beguwa?". bbc hausa. 16 May 2016. Retrieved 16 August 2021.
- ↑ Ibrahim, Aminu (4 February 2018). "Jerin muhimman kalmomin hausa 20 da ma'anar su a harshen turanci". legit hausa. Retrieved 16 August 2021.
- ↑ "Porcupine spines are enough to deter the most dangerous of predators". bbc.co.uk. 18 December 2019. Retrieved 16 August 2021.