Fuad Shukr
Fuad Shukr | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Al-Nabi Shayth (mul) , 15 ga Afirilu, 1961 |
ƙasa | Lebanon |
Mutuwa | Haret Hreik (en) , 30 ga Yuli, 2024 |
Yanayin mutuwa | kisan kai (airstrike (en) ) |
Karatu | |
Makaranta | Imam Hossein University (en) |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | militant (en) da ɗan siyasa |
Mamba | Hezbollah |
Aikin soja | |
Ya faɗaci |
Israeli occupation of Southern Lebanon (en) 2006 Lebanon War (en) Israel–Hamas War (en) |
Imani | |
Addini | Musulunci |
IMDb | nm16397408 |
Fuad shukr, (Larabci: فؤاد شكر; 15 an haife shi a watan Afrilu shekarar alif dari tara da sittin da daya miladiyya 1961, - ya mutu 30 ga watan Yuli 2024; wani lokaci yakan rubuta Fouad Shukar kuma wanda ake yi masa lakabi da Al-Hajj Mohsen ko Mohsen Shukr)[1]ya kasance shugaban mayakan Lebanon wanda babban memba ne na Hezbollah, Shukr babban jigo ne na soja a kungiyar tun farkon shekarun 1980. Sama da shekaru arba'in ya kasance daya daga cikin manyan sojojin kungiyar kuma ya kasance mai baiwa shugabanta Hassan Nasrallah shawara kan harkokin soji.
Shukr, a cewar leken asirin Isra'ila, ya kasance jigo wajen mika tsarin jagorancin Iran ga makamai masu linzami na Hezbollah[2]. An yi imanin ya taka rawa a harin bam na barikin Beirut na 1983, [3] wanda ya kashe sojojin Amurka 241, da na Faransa 58, fararen hula shida da maharan biyu. Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Shukr a matsayin wani ɗan ta'adda na musamman da aka zayyana a duniya a cikin 2013. [4]
A ranar 30 ga watan Yuli shekarar dubu biyu da ashirin da hudu (2024), an kashe Shukr a wani harin da Isra'ila ta kai a Beirutt saboda zarginsa da kai harin Majdal Shams kwanaki uku da suka gabata, wanda ya kashe yara 12.[5]
Rayuwa
Shukr, an haifi Shukr a ranar 15 ga Afrilu 1961, A kauyen Al-Nabi Shayth, a gabashin kasar Labanon, wanda kuma shi ne mahaifar shugaban kungiyar Hizbullah, Abbas al-Musawi. Bayan kafuwar kungiyar Hizbullah, kauyen ya zama daya daga cikin sansanonin da ke karkashinta. An yi imanin cewa gidan Shukr da ke Al-Nabi Shayth shi ne na karshe da aka sani da Ron Arad matukin jirgin yakin Isra'ila da ya bace a kasar Labanon a shekarar 1986. Shukr ya yi karatunsa na soja a jami'ar Imam Hossein da ke Tehran.[6]
Manazarta
Preview of references
- ↑ [1]
- ↑ "Israeli strikes on Beirut and Tehran could intensify a regional war". The Economist. ISSN 0013-0613 . Archived from the original on 1 August 2024. Retrieved 1 August 2024.
- ↑ https://web.archive.org/web/20240801140352/https://www.economist.com/middle-east-and-africa/2024/07/31/israeli-strikes-on-beirut-and-tehran-could-intensify-a-regional-war
- ↑ https://www.aljazeera.com/news/2017/10/11/us-offers-rewards-fortalal-hamiyah-and-fuad-shukr
- ↑ https://gulfnews.com/world/mena/source-close-to-hezbollah-says-body-of-top-commander-killed-in-israeli-strike-found-1.103679150
- ↑ https://www.ynet.co.il/news/article/rj2w1jlkc