Iftar (Budar Baki)
Iftar | |
---|---|
Iftar shi ne yin buda-baki a lokacin mangariba da al'ummar musulmi ke yi a cikin watan Ramadan a lokacin addhan (kiran salla) na sallar magriba[1].
Wannan shi ne abincinsu na biyu; azumin ranar ramadan yana farawa ne bayan an gama sahur kuma ana ci gaba da yin sa’o’in hasken rana, yana karewa ne da faduwar rana da buda baki.[2]
Yadda ake gudanar da Iftar (Buda Baki)
Iftar yana daya daga cikin muhimman abubuwan da ake yi lokacin watan ramadan, kuma an fi yinsa a tarin jama'a, da yan'uwa musulmai su zauna su ci su sha a tare wanda haka ke kara dankon zumunci a tsakanin[3]. A al'adance ana cin dabino guda uku domin buda baki, a yi koyi da Annabin Musulunci, Muhammadu (SAW) wanda ya yi buda baki ta wannan hanyar, amma wannan ba wajibi ba ne. Musulmai sun yi imanin cewa ciyar da wani buda baki a matsayin sadaka yana da lada sosai kuma Annabi Muhammadu ne ya yi koyi da hakan.[4][5]
Manazarta
Preview of references
- ↑ Fieldhouse, Paul (1 April 2017). Food, Feasts, and Faith: An Encyclopedia of Food Culture in World Religions [2 volumes] (illustrated ed.). ABC-CLIO. p. [1]. ISBN 9781610694124. Retrieved 27 May 2019.
- ↑ "Iftar buffet culture on rise in twin-cities". Daily Times. 2022-04-19. Retrieved 2022-12-14.
- ↑ Barr, Sabrina (11 May 2019). "RAMADAN 2019: HOW TO FAST RESPONSIBLY DURING THE MUSLIM HOLY MONTH". independent.co.uk. Independent. Retrieved 27 May 2019.
- ↑ "Ramadan 2019: Why is it so important for Muslims?". aljazeera.com. Aljazeera. 5 May 2019. Retrieved 27 May 2019.
- ↑ Setyorini, Tantri (22 May 2018). "Doa berbuka puasa berikut arti dan kajian dalilnya". Merdeka. merdeka.com. Retrieved 27 May 2019.