Masallacin Annabi

Masallacin Annabi
المسجد النبوي
Wuri
Ƴantacciyar ƙasaSaudi Arebiya
Province of Saudi Arabia (en) FassaraMedina Province (en) Fassara
Babban birniMadinah
Coordinates 24°28′06″N 39°36′39″E / 24.4683333°N 39.6108333°E / 24.4683333; 39.6108333
History and use
Foundation stone laying ceremony 622
Addini Musulunci
Suna Muhammad
Maximum capacity (en) Fassara 600,000
Karatun Gine-gine
Style (en) Fassara Islamic architecture (en) Fassara
Tsawo 105 m
Parts Hasumiya: 10
Masallacin Annabi

Masallacin Annabi (Larabci ألمسجذ النبوي Al-Masjid An-Nabawi) Masallaci ne a birnin Madina na kasar Saudiyya, wanda Annabi Muhammad (S.A.W) ya kafa ginin shi, kuma shine masallaci na uku da aka gina a tarihi. Yana kuma ɗaya daga cikin masallatai da sukafi girma a duniya. Shine kuma waje mafi tsarki na biyu a Musulunci bayan masallacin Harami (ka'aba) dake birnin Makka na kasar ta Saudi Arabiya. Masallacin koda yaushe a bude yake domin aiwatar da aiyukan bauta ga musulmai.

Asalin wajen shine gidan Annabi (s.a.w) , anan ya zauna bayan yayi hijira daga maka zuwa birnin na Madina a shekarar 623 Miladiyya. Shine kuma ya assasa gina shi. Asalin masallacin budadden gini ne. Masallacin ya kasance waje ne na rayuwar al'uma kuma wajen Shari'a sannan kuma Makaranta ta koyar da addinin Musulunci. Asannu a hankali sarakunan musulunci ne sukai ta kokari wajen fadada shi da kara masa gyara har yakai kyakkyawa kamar yadda yake a yanzu. Shine waje na farko a yankin larabawa da aka fara sakama hasken wutar lantarki. Masallacin na karkashin hukumar dake kula da masallatai biyu masu tsarki ta kasar Saudiyya. Masallacin yana a tsakiyar birnin Madina, akwai manyan Hotel-hotel da tsofaffin kasuwanni a kewaye da shi. Babban waje ne na aiwatar da aikin umara ga mahajjata da masu ziyarar Umara.

Bayan fadada shi ne da daular Umaiya tayi karkashin sarkin daular Kalifa Al-Walid I, sai ya hado harda makwancin sa (S.A.W) da wasu Sahabbai nasa guda biyi (kalifofin Khulafa'hur-Rashidun na farko da na biyu). Daya daga cikin manyan sanannun gurare a masallacin shine babbar koyariyar Hasumiya wadda ananne daidai dakin Ummuna Ai'sha (matar Annabi (s.a w). A ranar 19 ga watan Maris ne hukumomi a kasar Saudiyya suka bayyana sanarwar rufe kofofin masallacin tare da hana yin dukkan wasu aiyuka na ibada da taruwar jama'a sakamakon kamari da annobar cutar Covid-19 tayi ma duniya.[1]

Tarihi

Tarihin farko

Hoton masallacin annabi.

Annabi Muhammad (s.a.w) ne ya gina masallacin a Madina bayan hijirar sa a shekarar 622miladiyya. Yana tafiya a kan dokin sa maisuna Qaswa sai ya zo daidai inda masallacin yake a yanzu. Asalin gurin mallakin wadansu mutanene Sahal da Suhail, wajene da ake busar da dabino, daga baya kuma aka maidashi makabarta. Annabi (s.a.w) yaki karbar filin a matsayi sadaka, sai ya sayi filin kuma yakai tsawon wata bakwai kafin a kammala ginin shi. Misalin tsawon masllacin shine, mita 30.5 × 35.62 ( kafa 100.1 × kafa 116.9) , an rufe shi da ganyen kwakwa sa kasa tsawon mita 3.60 (kafa 11.8). Kofofi ukun nasallacin sune Bab-al-Rahma daga kudu sai Bab-al-Jibril daga yamma sai kuma Bab-al-Nisa daga bangin gabas.

Bayan kammala yakin Khaibar an fadada masallacin da mita 47.32 (kafa 155.2) daga ko wanne bangare. A lokacin Kalifa na farko wato Sayyadina Abubakar yabar masallacin haka amma daga baya lokacin kalifancin Sayyadina Umar sai ya rusa sauran gidajen dake makotaka da masallacin banda gidan Ummuna Aisha domin kara fadadashi. Sabon gyaran ya kasance kamar haka, mita 57.49 × mita 66.14 (kafa 188.6 × 217.0). Anyi amfani da busaaahen tabo da laka wajen gina katangar masallacin. Umar kuma ya kara da gina wadansu kofin ciki harda kofar Al-Bukaiha.

Kalifa na uku wato Sayyadina Usman, ya rushe masallacin a shekara ta 649miladiyya. Inda ya dauki tsawon wata goma domin gina masallacin, ananne kuma ya daidaita fuskar sa ta koma kallon Makka. Ga yadda nasa aikin ginin ya kasance, mita 81.40 × mita 62.48 (kafa 167.1× kafa 205.3). Dukkan kofofin da sunayen su basu canza ba.

Shekarun tsaka tsakiya

Masallacin Annabi a zamanin daular Usmaniyya, karni na 19.

A shekara 707 Kalifa na daular Umayya Al-Walid Ibn Abdal-Malik ya sake gina masallacin. Ya dau shekara uku kafin aikin ya kammala. An kara fadin masallacin da sukwaya 5094.

Hoton babbar Hasumaya ta masallacin Annabi lokacin ziyarar Rechard Frances Burton (dan kasar Birtaniya mai nazari kan yanayin duniya da halitta, kuma mai fassara, marubuci, soja, mai jawabi, mai daukar hoto, mai nazarin yarurruka kuma jami'in Diflomasiyya) a 1850.

Kalifan Abbasiyya wato Kalifa Al-Mahdi ya kara tsawon masallacin daga arewa da mita 50 (kafa 160). An rubuta sunan sa a katangar masallacin. Ya kuma yi kokarin ya matsar da hawan mimbarin zuwa hawa shida amma daga bisani sai ya fasa.

An gina babbar hasumaya a kan raudha da ta hado daga kudu maso gabashin kwanar masallacin. An gina ta a 1837m. Daga nan ake kiran ta da Koriyar Hasumiya

Sultan Abdul Majid I ya dauki shekaru goma sha uku wajen sake ginin masallacin, wanda aka fara a 1849. Anyi amfani da jan bulo wajen aikin sake ginin masallacin. An kara fadada daben da tsawon murabba'in sukwaya mita 1293. An kuma rubuta ayoyin Alkur'ani a kan katangun masallacin. An kuma gina makaranta wato Madrasah domin koyar da Alkur'ani.

Saudiyya

Lokacin da Sarki Saud bin Abdul-Aziz ya karbe Madina, ya dauki kudiri tare da aiwatar dashi. Kudirin kuwa shine na sake gina Masallacin tare da gyara da goge dukkannin abubuwan da zasu kawo matsala ga tauhidi, wato bidio'in da akayi kamar gyra ginin da akayi akan kabarin annabi tare da hana mutane yin sallah da adduo'i a wajen.

Bayan kafa masarautar Saudi Arabiya a 1937, masallacin ya fuskanci gyare gyare da dama kamar samar da hanya inda aka yanki wani bangare na shi. Da kuma karin hasumayoyi da samar da dakin karatu na litattafan musulunci.

A shekara 1974, Sarki Faisal ya kara fadin masallacin da sukwaya mita 40,440. An kuma kara fadada harabar sa a zamanin sarki Fahad a 1985. Lokacin da aka kammala aikin masallacin ya kai fadin kafa miliyan 1.7.

Anyi sanarwar fara aikin sabon gyara a masallacin na dalar Amurika biliyan $6b. a shekarar 2012. Idan an kammala aikin masallacin zai dauki adadin mutane miliyan 1.6.

Tsarin ginin

Raudah

Babbar Hasumaya

Mihirabi

Mimbari

mimbarin masallaci Annabi

Hasumaya

Hotunan masallacin Annabi

wata kofa ta shiga
Saitin Alkibla
babbar kofar shiga
masallacin Annabi da dare

Preview of references

  1. pic.twitter.com/6Dvoi0tAUc