Nelson Enwerem

Nelson Enwerem
Rayuwa
Haihuwa Jihar Abiya, 2 ga Augusta, 1995 (29 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Kwalejin Gwamnati Umuahia
Jami'ar Calabar
Matakin karatu Digiri
Harsuna Turanci
Harshen, Ibo
Sana'a
Sana'a model (en) Fassara, Mai tsara tufafi, interior designer (en) Fassara da hairdresser (en) Fassara
Imani
Addini Kiristanci
Nelson Enwerem

Nelson Enwerem da aka sani da laƙabin Prince, ɗan asalin Najeriya ne kuma mai aikin ado da kwalliya wanda ya ci gasar Mista Najeriya, a shekarar 2018 Ya wakilci Najeriya a gasar Mister World 2019 kuma an sanya shi cikin zababbu 26. A ranar 19 ga watan Yulin shekarata 2020, ya zo a matsayin mutum na uku da suka shiga cikin gasar Big Brother Naija karo na 5 kuma ya kare a matsayi na tara.

Tarihin Rayuwa

Enwerem an haife shi kuma ya girma a Aba, jihar Abia . Ya tafi Kwalejin Gwamnati ta Umuahia don karatun sakandare, kafin ya wuce zuwa Jami'ar Calabar inda ya yi karatu a tsangayar kimiyyar lissafi. Yayin da yake cikin jami'a, Enwerem yayi takara kuma yaci gasar Face of University Nigeria a shekarar 2016.

Aiki

Mr Nigeria 2018

A cikin shekarar 2018, Enwerem ya fafata kuma ya lashe gasar kyau ta maza mai suna Mr Nigeria 2018 wadda aka gudanar a ranar 28 ga watan Oktoban shekarar 2018 a Silverbird Galleria, Victoria Island, Lagos, Nigeria. Ya kuma lashe kyautar Mafi kyawun baiwa a gasar. Bayan haka, Enwerem ya sami damar wakiltar Najeriya a gasar maza ta duniya wato Mister World 2019.

Iyali

Enwerem ya fito ne daga garin Umuebie, Ugirinna, Isiala Mbano, jihar Imo, Najeriya kuma dan gidan sarauta ne . Mahaifinsa wato HRH Eze Leo Mike Enwerem, Ebi I shi ne sarkin garin Umuebie, Ugirinna Isiala Mbano. Mahaifiyarsa kuma sunanta Ugoeze Catherine Chika Enwerem.

Finafinai

Talabijan

Shekara Take Matsayi Bayanan kula
2020 Babban Brotheran'uwan kakar 5 Kansa Gaskiya nuna

Manazarta

  • Nelson Enwerem on Instagram