Yawon Bude Ido ilimi ne dakan sanar da kuma ganin abunda mutum bai sani ba, ko ya ji ana faɗa bai taɓa ganin shi ba, yawon bude ido na karawa mutum ilimi akan abinda bai sani ba kuma ya bada nishaɗi da farin ciki a lokacin da aka gudanar da shi. A lokutan baya zamu iya cewa kusan turawa ne sukafi maida hankali wajen yawon buɗe ido, to amman yanzun zamu iya cewa ko ina an maida hankali kan yawon buɗe ido.