Eskor Toyo

Eskor Toyo
Rayuwa
Haihuwa Oron, 1929
ƙasa Najeriya
Mutuwa Calabar, 7 Disamba 2015
Karatu
Makaranta University of London (en) Fassara
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a mai falsafa, marubuci da university teacher (en) Fassara
Employers Jami'ar Maiduguri

Eskor Toyo (an haifi Asuquo Ita ;[1] 1929 – 2015) ya kasance masanin Marxism ne na Najeriya, marubuci kuma malami.[2] Har zuwa rasuwarsa, Farfesa ne a fannin tattalin arziƙi a Jami'ar Calabar.[3]

Tarihin Rayuwa

An haife shi a shekarar 1929 a garin Oron na jihar Akwa Ibom, Eskor ya yi karatu a Calabar da Legas. Yayin da yake aji ɗaya a shekarar 1945, ya samu takardar shedar makarantar Cambridge da ta Cambridge Higher School Certificate wanda ya samu.[4] Bayan ya sami Difloma a fannin Gudanar da Jama'a, ya wuce Jami'ar London inda ya sami digiri na ɗaya a fannin tattalin arziki. Eskor ya ci gaba da karatunsa inda ya kamalla digirinsa na biyu a fannin Tsarin Tattalin Arziƙi na Ƙasa, MSc da kuma digirin digir-gir, PhD a fannin tattalin arziƙi.[4]

A matsayinsa na malami, Eskor ya koyar da ilimin tattalin arziki a wasu jami'o'in; Turai da Najeriya kafin ya zama shugaban sashen nazarin tattalin arziki a jami'o'in Maiduguri da Calabar.[4]

Eskor ya kasance ɗaya daga cikin jiga-jigan waɗanda suka kafa rusasshiyar jam'iyyar Marxist-Leninist Socialist Workers and Farmers Party of Nigeria.[5][6] Bayan fama da ciwon shanyewar jiki, ya rasu ne ranar 7 ga watan Disamba 2015 a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Calabar da ke birnin Calabar.[7]

Manazarta

  1. "Buhari pays ultimate tribute to Eskor Toyo". The News Nigeria. 3 March 2016. Retrieved 4 March 2016.
  2. Patrick Okedinachi Utomi (2002). To Serve is to Live: Autobiographical Reflections on the Nigerian Condition. Spectrum Books. ISBN 978-978-029-144-0.
  3. Leadership Editors (29 December 2015). "Professor Eskor Toyo (1929–2015)". Leadership Newspaper. Retrieved 19 January 2016.
  4. 4.0 4.1 4.2 "Eskor Toyo: Exit of a renowned scholar and activist". The Sun Newspaper. 23 December 2015. Archived from the original on 25 January 2016. Retrieved 19 January 2016.
  5. Edwin Madunagu (2001). The Making and Unmaking of Nigeria: Critical Essays on Nigerian History and Politics. Clear Lines Publications.
  6. Edwin Madunagu; Biodun Jeyifo (2006). Understanding Nigeria and the new imperialism: essays 2000–2006. Clear Lines. ISBN 978-978-38525-1-8.
  7. Todo, Tina (10 December 2015). "Eskor Toyo dies at 85". The Guardian Newspaper. Calabar. Retrieved 19 January 2016.

Littafi Mai Tsarki

Hanyoyin haɗi na waje