Isabelle Tokpanou
Isabelle Tokpanou | |||
---|---|---|---|
District: East (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Kribi (en) , 27 Nuwamba, 1936 (87 shekaru) | ||
ƙasa | Kameru | ||
Karatu | |||
Harsuna | Old French (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa, university teacher (en) da physiologist (en) | ||
Employers |
Jami'ar Lomé Jami'ar Yaoundé | ||
Kyaututtuka | |||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Cameroon People's Democratic Movement (en) |
Isabelle Marie Ndjole Assouho (an haife ta a ranar 27 ga watan Nuwamba a shekara ta alif 1936, a cikin Kribi) 'yar siyasar Kamaru ce. An zaɓe ta a matsayin ‘yar majalisar dattawa mai wakiltar yankin Gabas a zaɓen ‘yan majalisar dattawa na farko da aka gudanar a ranar 14 ga watan Afrilun 2013.
A matsayinta na Farfesa na jami'a, ita ce shugabar hukumar Yaounde kuma Aminatou Ahidjo ta maye gurbinta a ranar 29 ga watan Yuni[1][2] [3]
Ta yi shekaru biyar tana Sakatariyar Jiha a ma'aikatar ilimi ta ƙasa (yanzu ma'aikatar ilimin sakandare). Tana da aure tana da ‘ya’ya huɗu.[4]
Ilimi da aiki
Mai riƙe da Baccalaureate ta samu a shekarar 1957, Tokpanou ta ci gaba da karatun digiri a Faransa inda ta kammala karatun digiri a kimiyyar dabi'a a shekarar 1963, DEA a fannin ilimin halittar dabbobi a shekarar 1975 da PhD a fannin ilimin halittar dabbobi a shekarar 1978, duk sun samu a Jami'ar Poitiers.
A shekarar 1963, ta fara aikinta na koyar da manyan makarantu a Benin, Ivory Coast da Faransa har zuwa 1975, lokacin da ta zama mataimakiya a fannin ilimin halittar dabbobi a Jami'ar Benin, a yau Jami'ar Lome[5] a Togo.
A cikin shekarar 1978, ta shiga Jami'ar Yaounde kuma a cikin 1980, ta zama malama a Faculty of Sciences. Bayan haka, ta zama shugabar Majalisar Dokoki ta ƙasa na tsawon shekaru goma bayan ta zama Sakatariyar Gwamnati a Ma’aikatar Ilimi.
Siyasa
Isabelle Tokpanou 'yar gwagwarmaya ce ga CPDM inda ta kasance mamba a kwamitin tsakiya. An zaɓe ta a matsayin ‘yar majalisar dattijai ta yankin Gabas a zaɓen 2013 na majalisar dattawan Kamaru.
Manazarta
Preview of references
- ↑ Mbohou, Azize (23 March 2020). "Sénat : en alerte maximale !". Cameroon Tribune (in Faransanci). Retrieved 2020-08-27.
- ↑ "Cameroun: Isabelle Tokpanou - L'Antilope qui fait de la résistance". AllAfrica. 4 December 2007.
- ↑ Atangana, Adeline (29 June 2016). "Cameroun: Paul Biya nomme Aminatou Ahidjo PCA du Palais des Congrès a Yaoundé !". Cameroon Info (in Faransanci). Retrieved 2018-08-17.
- ↑ Atangana, Adeline (29 June 2016). "Cameroun: Paul Biya nomme Aminatou Ahidjo PCA du Palais des Congrès a Yaoundé !". Cameroon Info (in Faransanci). Retrieved 2018-08-17.
- ↑ Flore, Germaine (29 April 2013). "Sénatoriales 2013, les résultats sont connus". Archived from the original on 2017-09-09. Retrieved 2018-08-17.