Laurens Van der post
Laurens Van der post | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Philippolis (en) , 13 Disamba 1906 |
ƙasa | Afirka ta kudu |
Mutuwa | Landan, 16 Disamba 1996 |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Ingaret Giffard (en) |
Yara | |
Ƴan uwa |
view
|
Karatu | |
Makaranta | Grey College (en) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | Marubuci, marubuci, marubin wasannin kwaykwayo, ɗan jarida da Manoma |
Kyaututtuka | |
Aikin soja | |
Fannin soja | British Army (en) |
Digiri | colonel (en) |
Ya faɗaci | Yakin Duniya na II |
IMDb | nm0886394 |
Sir Laurens Jan van der Post, CBE (13 ga a watan Disamba shekara ta 1906 zuwa 15 ga watan Disamba shekara ta 1996) [1] [2] marubuci ne ɗan Afirka ta Kudu ne, manomi, soja, malami, ɗan jarida,me fafutuka saboda yancin ɗan adam, masanin falsafa, mai bincike kuma masanin kiyayewa. An lura da shi saboda sha'awar Jungianism da mutanen daji na Kalahari,sanin sa akan abubuwan da suka faru a lokacin yakin duniya na biyu, da kuma dangantakarsa da manyan mutane irin su Sarki Charles III da Firayim Minista na Birtaniya Margaret Thatcher. Bayan mutuwarsa, an yi ta cece-kuce kan ikirarin cewa ya yi karin gishiri a bangarori da dama na rayuwarsa, da kuma yadda ya yi lalata da wata yarinya ‘yar shekara 14 da haihuwa da kuma yi mata ciki.[3]
Tarihin Rayuwa
SHEKARUN FARKO DA ILIMI
An haifi Van der Post a wani karamin gari na Philippolis a yankin Orange river, sunan bayan yakin Boer na Burtaniya ga abin da a baya ya kasance Afrikaner Orange Free State a inda ya kasance Afirka ta Kudu a yau.[4] Mahaifinsa, Christiaan Willem Hendrik van der Post (shekarar 1856 zuwa shekarar 1914), dan Hollander daga Leiden, ya yi hijira zuwa Afirka ta Kudu tare da iyayensa kuma ya auri Johanna Lubbe a shekarar 1889. Van der Posts yana da yara 13, inda Laurens shine na 13. Da na biyar, Christiaan, lauya ne kuma dan siyasa wanda ya yi yaki a yakin Boer na Biyu da Birtaniya. Bayan Yaƙin Boer na Biyu, an kai babban Christiaan tare da danginsa zuwa Stellenbosch, inda aka samu cikin Laurens. Suka koma Philippolis, a cikin yankin Orange River, inda aka haife shi a shekarar 1906.
Manazarta
- ↑ Pottiez, Jean-Marc (17 December 1996). "Obituary: Sir Laurens van der Post". The Independent. Retrieved 12 September 2021.
- ↑ Lawrence Van Gelder (17 December 1996). "Laurens van der Post, 90, Dies; Thoughtful Man of Adventure". The New York Times. p. B 12. Retrieved 2 August 2021.
- ↑ Gray, Chris (18 October 2012). "Another knight with a tarnished reputation". Oxford Mail. Retrieved 24 October 2022.
- ↑ "A Prophet Out of Africa". The Times. 17 December 1996. Archived from the original on 7 September 2006.