Rukunnan Musulunci

Rukunnan Musulunci
obligation (en) Fassara
Bayanai
Facet of (en) Fassara Musulunci

Rukunnan Musulunci Biyar (arkān al-Islām, larabci أركان الإسلام; ko arkān al-dīn, larabci أركان الدين, Rukunnan addini, Shika-shikan addini) abubuwa ne ko ayyuka waɗanda ginshikai ne, guda biyar a Musulunci, wadanda wajibai ne akan kowane mai imani, kuma sune farkon ginshikin rayuwar Musulmi. Suna nan tattare a shahararren hadisin nan na mala'ika Jibril.[1][2][3][4]

Shia, da Ahmadiyya, da Sunni dukkanin su sun yarda da muhimman bayani da ayyukan wadannan abubuwan,[5][2] amma Shi'a basa kiran su da irin wannan sunan (see Ancillaries of the Faith, na Twelvers, da kuma Seven pillars of Ismailism). Sune suka hada rayuwar musulmi, sallarsa, taimakawa gajiyayyu, tsarkake kai daga zunubbai, da aikin hajji,[6][7] ga wanda yake da ikon zuwa.[8]

Shahada: (Imani)

Shahada ita ce miƙa wuya da tabbatar da Imani da bada gaskiya dake yarda da cewar babu wani abun bauta idan ba (Allah) ba, kuma Annabi Muhammad Manzon Sa ne, Kalman shahada dai rukuni ne na farko daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar, wanda wajibi ne sosai mutum ya kiyaye ta , tana shigar da mutum cikin Musulunci in har ya furta , kuma ya kudur ce a zuciyar shi ,kuma yayi aiki da ma`anan abinda ya firta, kuma tana fitar da Mutum daga Musulunci idan ya saɓa ma`anar kalman ta hanyan yin saɓo ko shirka ko ya aikata wani aiki dake fitar da mutum daga Musulunci

Kalmar da kuma Ma`anarta

Kalma itace kamar haka:- Na shaida babu abinda bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad Manzo n Allah ne.

 Ma`anarta shine ka yarda akan karan kanka ba tilasta ka akayi ba cewa Allah shi kaɗai zaka bautamawa , shine ka tsayar da Tauhidi guda uku Rububiyya da Uluhiyya da Asma`i wassifat , kuma  baza ka haɗa shi da kowa ba a gurin bauta , wato baza kayi Shirka ba ko Tsafi ko wani nauyin na hakan, kuma kaji ka yarda cewa Annabi Muhammad manzan Allah. Ma`ana ɗan aike ne daga Allah. Ma`ana duk abinda Annabi Muhammad yace zaka yarda kuma ka gasgata ,abinda yayi umurni dashi kuma ko yayi hani, zaka aika ta sau da kafa.  

.[9] Jawabi ne da yake a tsare, kuma ana furta shi ne da Larabci: lā ʾilāha ʾillā-llāhu muḥammadun rasūlu-llāh, (لَا إِلٰهَ إِلَّا الله مُحَمَّدٌ رَسُولُ الله) "Babu abun bautawa da gaskiya sai Allah (kuma) Annabi Muhammad Manzon Allah ne. Furta wannan jawabin nada muhimmanci sosai, Kafin mutum yazama Musulmi, ko ya dawo musulunci.[10]

Salah: (Sallah)

Sallah (ṣalāh) itace bautar musulmai, Sallah ta kunshi yin salloli biyar kamar yadda Sunnah tazo dasu; sunayensu akan lokutan Amfani: Fajr (Subhi), Dhuhr (rana), ʿAṣr (Yamma), Maghrib (Almuru), da kuma ʿIshāʾ (dare). Sallar Fajr ana gudanar da ita ne kafin fitowar(tasowar) rana, Dhuhr kuma ana yinta ne a tsakiyar rana, bayan rana yayi zawali, Asr kuma da yammaci ake yinta kafin faduwar rana, Maghrib da almuru bayan rana ya fadi, sannan sai sallar Isha'i da akeyinta acikin dare. Duk wadannan salloli anayinsu ne ta hanyar kallon Kaaba a Mecca daya samar da muhimmin ginshiki a cikin alumman Musulmi. Musulmi sai sun wake jiki kafin yin Sallah; wannan wankin ake kira da wudu

Zakāh: (Zakkah)

Zakkāh Zakka rukuni ne daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar ana bayar da wani sashi ne na dukiyar mutum idan dukiyar ta kai nisabi.

Sawm: Azumi

Azumi rukuni ne daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar , ana kin cin abinci ne da kuma kin shan abun sha tin daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana , haka za`a tayi har sai anyi wata daya na watan Ramadan tukunnan aka sauke nauyin farillan. [11] ref>Al Kur'ani 2:196</ref> .[12][13]


Hajj: Aikin Hajji

Hajj itace ziyarar ibada dake faruwa a kowace watan musulunci na Dhu al-Hijjah zuwa Makkah. Kowani musulmi baligi dake da iko ya zama wajibi yayi aikin hajji a rayuwarsa koda sau ɗaya ne, Hajji rukuni ne daga cikin Rukannan Musulunci guda biyar ga wanda Allah ya bashi ikon zuwa ,ana yin aikin hajji ne kaɗai a makkah, kuma ba`a son mutum ya tafi aikin hajji alhali akwai bashi akan shi ko iyalansa na cikin wani hali ,ko kuma zasu shiga idan har ya tafi. .[14]

Manazarta

  1. "Pillars of Islam". Encyclopædia Britannica Online. Retrieved 2007-05-02.
  2. 2.0 2.1 "Pillars of Islam". Oxford Centre for Islamic Studies. United Kingdom: Oxford University. Archived from the original on 2009-02-11. Retrieved 2010-11-17.
  3. "Five Pillars". United Kingdom: Public Broadcasting Service (PBS). Retrieved 2010-11-17.
  4. "The Five Pillars of Islam". Canada: University of Calgary. Retrieved 2010-11-17.
  5. "The Five Pillars of Islam". United Kingdom: BBC. Retrieved 2010-11-17.
  6. Hooker, Richard (July 14, 1999). "arkan ad-din the five pillars of religion". United States: Washington State University. Archived from the original on 2010-12-03. Retrieved 2010-11-17. Unknown parameter |deadurl= ignored (|url-status= suggested) (help)
  7. "Religions". The World Factbook. United States: Central Intelligence Agency. 2010. Archived from the original on 2018-12-20. Retrieved 2010-08-25.
  8. Hajj
  9. From the article on the Pillars of Islam in Oxford Islamic Studies Online[permanent dead link]
  10. Matthew S. Gordon and Martin Palmer, ''Islam'', Info base Publishing, 2009. Books.Google.fr. 2009. p. 87. ISBN 9781438117782. Retrieved 2012-08-26.
  11. Al Kur'ani 2:183–187
  12. Al Kur'ani 33:35
  13. Fasting, Encyclopedia of the Qur'an (2005)
  14. Farah (1994), p.145-147


[[Category:Kalma shahada]