Tandi Mwape (an haife shi ranar 20 ga watan Yuli, 1996) shi ne ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Zambia wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya ga TP Mazembe da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Zambia.[1]
Sana'a/Aiki
Kulob
Bayan shafe shekaru da yawa a kasarsa ta Zambiya, Mwape ya koma kulob din TP Mazembe na Congo a watan Yulin 2019. Ya buga wasansa na farko a kungiyar kwanaki kadan bayan sanarwarsa, inda ya bayyana a cikin rashin nasara da ci 1-0 a gasar Rayon Sports a Kagame Interclub Cup.[2]
Ƙasashen Duniya
Mwape ya fara buga wasansa na farko a duniya a ranar 2 ga Yuni 2019 a bugun fanareti a kan Malawi a gasar cin kofin COSAFA.[3]