Wikipedia:Mahangar da ba son rai
Dukkan muƙalolin insakulofidiya dake a cikin Wikipedia ya zama tilas a rubuta su daga mahangar gaskiya da adalci, mahangar da ba son rai ko kuma fifita wani al'amari saboda wani dalili. Dole ne a ba kowane al'amari hakkinsa kamar yadda yake a sahihan hanyoyin samun bayanai, ba tare da dasashe wata mahangar ko kuma fifita wata ba.
![](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/e/ed/Wikipedia_scale_of_justice.svg/200px-Wikipedia_scale_of_justice.svg.png)
Rubutu daga mahangar da ba son rai, yana daga cikin muhimman ginshikan Wikipedia